in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin tsagaida bude wuta na Amurka da Rasha a kudancin Syria ya fara aiki
2017-07-10 10:51:57 cri
A jiya Lahadi ne shirin tsagaida bude wuta da kasashen Amurka da Rasha suka cimma ya fara aiki a sassan kudancin kasar Syria. Kafofin watsa labaran kasar sun ce shirin ya hada da sassan lardunan Sweida, da Daraa, da kuma Qunaitera.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya bayyana cewa kasashen biyu sun cimma matsaya game da kawo karshen kaddamar da hare hare a wadannan yankuna. Ya kuma ce yarjejeniyar da aka cimma idan har ta yi nasara, na iya zama ginshikin kawo karshen dauki ba dadi a wasu karin sassan kasar ta Syria.

Wannan shiri dai na tsagaita bude wuta, bangare ne na fadada matakai da aka amince za a dauka tun cikin watan Mayun da ya gabata a sassan kasar ta Syria hudu, ciki hadda yankunan kudancin kasar inda fada ke kara kazanta, matakin da ya sanya Amurka da Rasha cimma wannan yarjejeniya ta tsagaita bude wuta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China