in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na gwamnatin Sin ya bayyana fatan kasar game da shawarwarin neman sulhu kan batun Syria
2017-07-15 13:29:27 cri
Manzon musamman na kasar Sin dake kula da harkokin kasar Syria Xie Xiaoyan, ya ce kasar Sin na goyon bayan MDD da ke jagorantar aikin shiga tsakani domin warware batun Syria. Haka kuma, ta na son ba da gudummawa yadda ya kamata, domin cimma sakamako mai gamsarwa a yayin taron tattaunawar neman sulhu kan batun Syria.

Mr.Xie wanda ya bayyana haka a jiya Juma'a, ya ce kasar Sin tana sa ran za a cimma abubuwa da dama yayin tattaunawar na wannan karon, musamman ma a fannoni uku da suka hada da: kada a tattauna kan wadancan muhimman batutuwan da aka cika haifar da sabani tsakanin bangarorin da batun ya shafa kafin a samu fahimtar juna a tsakaninsu, kamata ya yi a tattauna kan wasu batutuwan da aka fi samu ra'ayin bai daya a kai.

Na biyu shi ne, akwai bukatar a tabbatar da yanayin tsagaita bude wuta a kasar Syria ta hanyar siyasa, a sa'i daya kuma, a dukufa wajen cimma sakamako kan shawarwarin neman sulhu, ta yadda za a karfafa gwiwar bangarorin da abin ya shafa har ma da na gamayyar kasa da kasa baki daya.

Na karshe shi ne, ya kamata gamayyar kasa da kasa su dukufa wajen kai zuciya nesa a tsakanin gwamnatin kasar Syria da bangarori masu adawa da ita, ta yadda za a gudanar da shawarwari a tsakaninsu cikin yanayi mai kyau, tare da samar da wasu kudurorin da za su dace da moriyar kasar da kuma al'ummominta baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China