in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattaunawa kan batun Syria na baya-bayan nan ya kare ba tare da wata gagarumar nasara ba
2017-07-15 13:05:02 cri
Manzon musammam na MDD kan batun Syria Staffan De Mistura ya sanar da cewa, an kammala zagayen tattaunawar zaman lafiya na baya-bayan nan kan batun Syria, ya na mai cewa zagaye na gaba zai zo a farko watan Satumba.

Staffan de Mistura wanda ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya da daddare, ya ce an kammala zagaye na 7 na tattaunawar, inda ya ce an dan samu karin ci gaba, domin babu wanda ya fice haka zalika babu matsala da aka samu.

Ya ce ya na jin cewa, mutanen da ya tattauna da su a wannan makon, na goyon bayan abun da suke son cimmawa.

De Minstura ya kuma sanar da cewa, za a fara sabon zageyen tattaunawar a farko watan Satumba.

Da yake bada amsa kan tambayar da aka masa game wata tawaga da Faransa ta kafa, de Mistura ya ce ya tuntubi ayarin sosai, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya samar kwanannan, kan yadda kasarsa za ta bada gudunmuwa ga aikin da MDD ta ke kan batun Syria.

Faransa ta kira jerin taruka da Rasha da kuma Amurka ciki har da Shugaba Donald Trump, inda shugaban na Amurka ya yi maraba da wannan yunkuri da zai taimakawa tattaunawar zaman lafiya a Syria, wanda alama ce dake nuna cewa Faransa za ta fara taka muhimmiyar rawa a tattaunawar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China