in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kada a jawo wa Syria baraka a yayin daidaita batun kasar, in ji manzon musamman na kasar Sin
2017-07-23 13:40:36 cri
Manzon musamman na kasar Sin kan batun Syria, Mr. Xie Xiaoyan, ya bayyana a jiya Asabar cewa, ya kamata a daidaita batun Syria a siyasance ba tare da jawo mata baraka ba.

Mr. Xie Xiaoyan ya fada a yayin da yake sulhuntawa a kwanan nan, gwamnatocin kasashen Syria da Iran sun jaddada cewa, a yayin da ake daidaita batun kasar Syria a siyasance, ya zama dole a kiyaye mulkin kan kasar da kuma cikakken 'yancinta, kuma duk wani matakin da aka dauka ya kamata ya taimaka ga cimma wannan buri. Don haka, ya kamata a dauki matakan da suka dace, don magance jawo wa kasar ta Syria baraka, abin kuma da ya samu amincewa daga kasar Sin.

Daga ranar 20 zuwa 23 ga wata, Mr. Xie Xiaoyan ya kai ziyara kasar Iran, inda ya yi shawarwari tare da jami'an gwamnati da kuma masana na kasar, inda kuma suka yi musayar ra'ayoyi a kan batun Syria. Ya ce, "Iran kasa ce mai muhimmanci a shiyyar, wanda kuma ke da tasiri sosai a kan batun Syria."

A game da batun yaki da ta'addanci, Mr. Xie Xiaoyan ya ce, kasar Sin ita ma kasa ce da batun ta'addanci ke addabarta, don haka take nuna rashin amincewa da kowane irin ta'addanci. Ya kamata kasa da kasa su hada karfi da karfe, don murkushe 'yan ta'adda a kasashen.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China