Wani jami'i a lardin Hebei na kasar Sin ya ce a shirye lardinsa yake wajen yin muhimmiyar hadin gwiwa da jahar Kaduna dake arewacin Najeriya.
Wang Xiaodong, mataimakin gwamnan lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ziyara a jahar Kaduna, domin rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da gwamnan Kadunan Nasiru El-Rufai.
Makasudin yin hadin gwiwa a tsakanin Hebei da Kaduna shi ne, domin kulla kyakkyawar dangantaka a tsakanin bangarorin 2 da kuma kafa masana'antu a jahar ta Kaduna.(Ibrahim)