in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar bakin wake ya hallaka a kalla mutane 12 a Maiduguri
2017-07-17 19:46:37 cri
A kalla mutane 12 ne suka hallaka, sakamakon aukuwar wasu tagwayen hare haren kunar bakin wake a birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, 'yan kunar bakin waken mata sun tada ababen fashewa a wani masallaci dake unguwar "London Chinki", lamarin da nan take ya sabbaba kisan mutane 10.

Daga bisani kuma aka ji tashin wasu ababen fashewar a Molai dake wajen birnin Maiduguri, wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla wasu mutanen biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China