Darakta janar na hukumar Sani Mashi, ya shedawa 'yan jaridu a Abuja babban birnin kasar cewa, akwai jahohi masu yawa a Najeriya da ake fargabar ambaliyar ruwan zata iya shafa.
Ya ce amfanin gona kadan ne za su iya jure ruwan sama mai yawa, ya kara da cewa, wasu amfanin gonar zasu iya mutuwa idan suka fuskanci mamakon ruwan na lokacin mai tsawo ba tare da samun hasken rana ba.
Hukumar ta kuma yi hasashen cewa, bayan daukewar daminar za'a iya fuskantar bushewar kasa.
Mashi ya ce hukumar tana gargadin cewa matsalar sauyin yanayin za ta iya shafar yanayin ruwan sama da ake samu a kasar.
Daraktan ya ce yayin da ake sa ran samun ruwan sama na dogon lokaci, sai dai ba'a samu ruwan a kan lokaci ba, kana an samu ruwan mai yawa a farkon lokaci a wasu sassan kasar.
A cewarsa, idan aka samu mamakon ruwan sama, hakan na nufin ruwan da aka sheka ya fi karfin bukatar da kasa take da shi.(Ahmad Fagam)