Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, 'yan kunar bakin waken mata sun tada ababen fashewa a wani masallaci dake unguwar "London Chinki", lamarin da nan take ya sabbaba kisan mutane 10.
Daga bisani kuma aka ji tashin wasu ababen fashewar a Molai dake wajen birnin Maiduguri, wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla wasu mutanen biyu.
To sai dai hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriyar ta ce mutane 8 ne aka tabbatar da rasuwar su, yayin da wasu karin mutanen 15 suka jikkata a yayin wannan lamari. Kaza lika a ranar Lahadin, sojoji sun harbe wasu mata 'yan kunar bakin wake su biyu dake dauke da ababen fashewa, yayin da suke kokarin tsallaka shingen tsaro da aka kafa a yankin Mammanti dake wajen birnin Maiduguri. (Saminu)