Wata sanarwa da Ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar jiya ta ce, Manufar wayar da kan ita ce, kyautata dabi'ar rashin shayar da nonon uwa zalla yadda ya kamata a Nijeriya, a daidai lokacin da ake bikin makon shayarwa na duniya.
Makon shayar na duniya mai taken 'shayarwa a tare mai dorewa' zai gudana ne daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Augusta.
Ma'aikatar ta ce Nijeriya kasa ce da ake shayar da nono uwa, wadda ke bin tsarin da kusan kashi 97, sai dai tsarin shayar da nonon uwa zalla bai samu wani ci gaba na azo a gani ba, la'akari da tashi da ya yi daga kashi 2 a shekarar 1990 zuwa kashi 17 a shekarar 2013.
Ta kara da cewa, rashin bayar da nonon uwa zalla yadda ya kamata a Nijeriya na da nasaba da rashin samun goyon baya daga mazaje da abokan zama da kuma ma'aikatan lafiya.
Sauran sun hada da jinkirin fara bada nonon da shawarwarin abokai tare da rashin ba iyaye dogon hutun haihuwa mai albashi.
Ma'aikatar ta ce samar da wani dandali da za a dade ana amfani da shi, wanda zai kunshi masana da masu ruwa da tsaki da matasa da kafafen yada labarai, zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta dabarun ciyar da jarirai da kananan yara. (Fa'iza Mustapha)