Kakakin sojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usman ne ya bayyana hakan a Abuja babban birnin kasar cewa, mayakan sun mika kansu ne ga runduna ta 120 ta sojojin Najeriya dake Goniri a jahar Borno.
Usman ya ce, a binciken da suka gudanar, sun tabbatar da cewa mayakan sun mika wuya ne sakamakon matsanancin halin da suka shiga, sannan sun gano cewa shugabannin kungiyar sun ba su gurguwar shawara.
Kakakin rundunar sojin ya ce mayakan sun yi danasanin jefa kansu cikin wannan muguwar dabi'a ta ta'addanci, kuma sun nuna gamsuwa da irin mu'amalar da sojojin Najeriya suka nuna musu a lokacin da suke hannun sojojin.
Sannan ya yi kira da sauran mayakan na Boko Haram da su amince su mika kansu domin kauracewa ayyukan ta'addanci da cutar da al'umma.
Usman ya ce akwai shiri na musamman da aka yi ga wadanda suka amince bisa radin kansu domin mika wuya, inda ya bayyana cewa ba za'a cutar da su ba.(Ahmad Fagam)