Sojoji a Najeriya sun kama mata da yaran mayakan Boko Haram
Hukumomin Soja a Najeriya sun bayyana cewa, dakarunsu sun yi nasarar damke mutane 37 da ake zaton mata da yaran mayakan Boko Haram ne, bayan da suka tsare daga hannun 'yan tada kayar bayan. Kakakin rundunar sojojin Najeriya Birgediya janar Sani Usman ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Alhamis cewa, an kama mutane talatin daga cikin wannan adadi ne ranar Talata a yankin Gujba dake jihar Yobe mai fama da tashin hankali, yayin da ragowar mutane 7 din kuma aka kama su a Kamuya dake jihar ta Yobe. Yanzu haka ana ci gaba da tantancesu da kuma asalin yankunan da suka fito. A hannu guda kuma, sojojin sun yi nasarar dakile hare-haren kunar bakin wake da ba su gaza hudu ba wadanda aka shirya kaiwa tsakanin ranar Lahadi zuwa Talata. A don haka, janar Usman ya yi kira ga jama'a da su taimaka wajen baiwa sojoji da sauran hukumomi tsaro muhimman bayanai da suka dace don hana mayakan Boko Haram din kai duk wasu hare-haren kunar bakin wake a cikin al'umma.(Ibrahim)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku