Rear Admiral Victor Adedipe, kwamandan hukumar sojin ruwa ta shiyyar gabashin kasar (FOC), shi ne yayi wannan gargadi a sansanin hukumar ta NNS Jubilee Base a kudancin jahar Akwa Ibom.
Ya ce kasancewar da yawa daga cikin jami'an rundunar suna cikin wasu kungiyoyi na shafukan sada zumunta na zamani wanda ya shafi na dangi ko abokai, amma ya hore su da su yi taka tsantsan game da irin abubuwan da zasu wallafa a shafukan.
Adedipe ya ce, a kwanannan an fitar da sabon tsari na ka'idojin da suka shafi mu'amala da kafafen sada zumunta na zami, ya ce ya kamata kowa ya neme su domin karantasu.
Babban jami'in sojin ruwan ya bukaci jami'an su kiyaye ka'idojojin hukumar da suka shafi yin ta'ammali da kafofin sadarwa na zamani.
Ya ce wallafa duk wani batu da ya shafi ayyukan hukumar a shafukan sada zumuntar zai iya samar da muhimman bayanai ga bata gari.(Ahmad Fagam)