Ma'aikatun kudi da na harkokin wajen kasar Amurka sun sanar da garkama wa wasu daidaikun mutane da hukumomi guda 18 na kasar Iran takunkumi, bisa zarginsu da goyon bayan Iran game da shirinta na makamai masu linzami da kuma aikata wasu laifuka a kasashe daban daban. (Tasallah Yuan)