in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka na aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran yadda ya kamata, in ji ministan kasar
2016-06-16 15:48:29 cri
Jiya Laraba 15 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya bayyana cewa, kasar Amurka tana aiwatar da harkokin da suka jibanci yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran daga dukkan fannoni yadda ya kamata, tana kuma ba wa bankuna da kamfanonin kasar da su yi hadin gwiwa tare da kasar Iran.

Kafin wannan, a ranar 14 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya ce, ko da yake kasar Amurka ta yi alkawarin kawar da takunkumin da ta kakaba wa kasarsa, amma har yanzu ba ta aiwatar da wannan mataki ba yadda ya kamata, shi ya sa, kasar Iran ta bukaci Amurka da ta dauki matakan da suka dace domin cika alkawarinta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China