in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadar shugaban Amurka: shirin tsawaita dokar kakabawa Iran takunkumi zai zama doka ko da rashin samun sa hannun shugaba Barack Obama
2016-12-16 10:42:28 cri
A jiya Alhamis 15 ga wata, fadar mulkin kasar Amurka ta bayyana cewa, ko da yake shugaban kasar Barack Obama bai sa hannu kan wani shirin tsawaita wa'adin dokar kakabawa Iran takunkumi ba, amma zai zama doka da kansa.

A wannan rana, fadar shugaban Amurka ta ba da sanarwar cewa, gwamnatin Obama tana ganin cewa, babu bukatar tsawaita wa'adin dokar kakabawa Iran takunkumi, amma a sa'i daya, ta jaddada cewa, tsawaita dokar ba zai dasa shinge ga gudanar da yarjejeniyar nukiliya ta Iran ba.

Bisa kundin tsarin mulkin kasar Amurka, idan shugaban kasar bai sa hannu ko nuna rashin amincewa kan kudurin da majalisar dokokin kasar ta zartas da shi cikin kwanaki 10 ba, wannan kuduri zai zama doka da kansa.

A wannan rana, sakataren harkokin waje na Amurka, John Kerry ya ba da sanarwar cewa, ko za a tsawaita dokar kakabawa Iran takunkumi ko a'a, ba zai yi tasiri ga Iran wajen soke takunkumin da aka kakaba mata a karkashin yarjejeniyar nukiliya ta Iran ba. Shi ma zai ci gaba da sa hannu kan umurnin soke takunkumi bisa yarjejeniyar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China