Bisa wannan daftari dai, kasar Amurka za ta sanyawa dukkanin masu hannu cikin shirin bunkasa makamai masu linzami na kasar Iran takunkumi, da kuma wadanda suka taba yin cinikayya da wadannan mutane.
Haka kuma, za ta sanyawa dakarun tsaron kasar Iran na IRGC takunkumi bisa zargin cewar suna da alaka da 'yan ta'adda. A sa'i daya kuma, za a karfafa matakan da za a dauka na safarar makamai zuwa kasar Iran.
Bisa gyaran fuska da aka yiwa daftarin da ya tanaji kakabawa kasar Rasha takunkumi kuwa, Amurka za ta sanyawa jami'ai da dama daga bangaren Rasha takunkumi, bisa laifukan da suka aikata na keta hakkin bil Adama, da karbar rashawa, da samar da makamai ga gwamnatin kasar Syria, da ba da taimako ga Rasha a fannin yin kutse ta kafar yanar gizo ko intanet, da kuma mu'amala da hukumar leken asiri da hukumar tsaro ta kasar Rasha.
Ministan harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya bayyana a yayin da yake halartar taron majalisar wakilai a ranar 14 ga wata cewa, ya amince da cewa, ya kamata kasar Rasha ta dauki alhakin laifinta, na tsoma baki cikin babban zaben Amurka, sai dai a daya bangaren ya yi kira ga majalisar dokokin kasar, da ta mai da hankali kan tsara daftarin da ya shafi wannan harka, domin gudanar da sauye sauye a yanayin diflomasiyya dake tsakanin Amurkar da kasar Rasha. (Maryam)