in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan Masar ta ce, ya kamata a inganta hadin gwiwa da Amurka ta fuskar yaki da ta'addanci
2017-07-17 11:59:46 cri

A jiya ne kakakin rundunar sojan kasar Masar ya ruwaito Mahmoud Hegazy, babban hafsan-hafsoshin sojan kasar yana jaddada cewa, kamata ya yi a inganta hadin gwiwa da kasar Amurka ta fuskar aikin soja, musamman ma ta fuskar yaki da 'yan ta'adda, a kokarin magance kalubalen fuskar tsaro da ake fuskanta a shiyya-shiyya.

A kwanan baya ne, Mahmoud Hegazy ya gana da Michael Garrett, babban jami'in rundunar sojan Amurka da ke ziyara a Alkahira, inda suka tattauna kan yadda za a zurfafa hadin gwiwa ta fuskar aikin soja a tsakanin kasashen 2, ciki had da atisayen soja cikin hadin gwiwa, yin mu'amalar bayanai na musamman, inganta karfin soja ta hanyar amfani da fasahohi na zamani da dai sauransu.

Kasar Masar ta shafe watanni da dama tana fuskantar babban kalubale ta fuskar yaki da ta'addanci. A ranar 10 ga wata ne kuma gwamnatin Masar ta sanar da tsawaita wa'adin dokar-ta-baci da watanni 3. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China