Cikin jawabinsa, shugaban Abdel-Fattah El-Sisi, ya ce kasarsa za ta ci gaba da kai hari ga mafakar 'yan ta'adda da wuraren da ake horar da su ba tare da yin wata-wata ba, ko suna cikin harabar kasar ko akasin haka.
Ya kara da cewa Gwamnati ba za ta kyale kashe-kashen da ake yi wa kiristoci Kifdawa na kasar ba.
A cewar jaridar Al-Ahram, alamu sun nuna cewa an kai hari ta sama a cikin kasar Libya, kuma tungar da aka kai wa harin na da alaka da harin da aka kai a kasar Masar kan wasu kiristoci Kifdawa a ranar Alhamis da ta gabata.(Bello Wang)