in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin Sin ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a Masar
2017-05-28 12:54:08 cri
A jiya Asabar, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yayin taron maneman labarai cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta'addanci mai tsanani da aka kai a lardin El Minya na kasar Masar. Ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping, firaministan kasar Sin Li Keqiang, da kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, sun riga sun aike da sakon alhini ga takwarorin aikinsu na kasar Masar, watau shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi, da firaminista Sherif Ismail, da kuma ministan harkokin wajen kasar Sameh Shoukry.

Haka zalika, Lu Kang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yaki da dukkan wasu aikace-aikace na ta'addanci, za ta kuma nuna goyon baya ga kasar Masar wajen kiyaye zaman lafiyar kasar, da kuma yaki da ta'addanci.

A ranar 26 ga watan nan ne dai wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hari kan wasu Kirista a lardin El Minya na kasar Masar, kuma ya zuwa yanzu, harin ya riga ya haddasa rasuwar mutane 28, yayin da 26 suka jikkata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China