in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta sanar wa kwamitin sulhu yadda ta kai hari ga 'yan ta'adda a Libya ta sama
2017-05-29 12:35:30 cri

A daren ranar 27 ga wata ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta ba da wata sanarwa, inda ta ce, a wannan rana, zaunanniyar tawagar Masar da ke MDD ta aikewa kwamitin sulhun wata wasika, inda ta yi bayani kan yadda rundunar sojan Masar ta kai hari ga 'yan ta'addan da ke kasar Libya ta sama a kwanan baya.

A cikin sanarwar, ma'aikatar harkokin wajen Masar ta ce, tawagar ta sanar da kwamitin sulhu na MDD cewa, a ranar 26 da 27 ga wata, bisa tanade-tanaden da ke cikin kundin tsarin MDD da kudurorin kwamitin sulhun dangane da yaki da ta'addanci, sojan Masar sun kai hari kan sansanin horas da 'yan ta'adda da ke birnin Derna a gabashin Libya.

Kana, rundunar sojan Masar ta ce, 'yan ta'addan da suka kai hari a Masar a kwanan baya, sun taba samun horo a Libya. Harin da Masar ta kaiwa 'yan ta'adda ta sama, mataki ne da ta dauka bayan da aka kai mata harin ta'addanci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China