Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron a ranar Lahadi, inda suka tattauna game da wasu muhimman batutuwa da suka shafi rikicin kan iyakoki ciki har da batun tashe tashen hankali a Libya.
Shugabannin kasashen biyu sun cimma matsaya game da daukar matakai na siyasa don warware rikicin kasar Libya, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar Masar Alaa Youssef ya tabbatar da hakan.(Ahmad Fagam)