Ministan kula da harkokin wasan motsa jiki na kasar Senegal, Matar Ba, ya tabbatar da cewa, cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wata mata, kana an garzaya da mutane kimanin 60 asibiti don ba su kulawa.
Wadan da suka ganewa idonsu faruwar lamarin sun ce, yayin da ake shiga karin lokaci na wasan, magoya-bayan kungiyar wasan kwallon kafa ta Ouakam ta fara jefa duwatsu kan magoya bayan dayar kungiyar, lamarin da ya tilasta masu kallo suka fita daga filin wasan. Daga bisani 'yan sanda sun harba hayaki mai sa kwalla, a kokarin tarwatsa magoya-bayan kungiyoyin yan wasan biyu, lamarin da ya jefa mutane cikin fargaba.
Yayin da masu kallo ke kokarin ficewa daga filin wasan, wata katanga ta rufta ba zato ba tsammani. Wani mutumin da ya ganewa idonsa ya ce, katangar ta rufta ne a kan jama'a, 'babu tantama akwai mutane da dama da suka mutu.'(Murtala Zhang)