in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gobara ta tashe a wani wurin ibada na kasar Senegal
2017-04-14 13:58:14 cri
Rahotanni sun bayyana cewa, gobara ta tashe a wani wurin ibada dake yankin Tambacounda na kudancin kasar Senegal a ranar Laraba, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 22, yayin da wasu sama da 100 suka jikkata.

Haka kuma, bayan tashin gobarar, iska ta hura wutar inda kama rumfuna kara da aka yi, lamarin da ya kara haddasa rasuwa da jikkatar mutane da dama.

Ya zuwa yanzu, ba a tabbatar da dalilin da ya haddasa tashin gobarar ba, sai dai, shugaban kasar Senegal Macky Sall da ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, ya bayyana cewa, ma'aikatan harkokin cikin gida za su je wurin domin fara binciken musababbin gobarar.

Rahotanni sun ce cikin ko wace shekara, a kan samu mutane masu dimbin yawa dake zuwa ibada a yankin daga kasar da kuma wasu kasashen yammacin Afirka.

An fara taron addinin na wannan karo ne tun daga ranar 8 ga wata, kuma bisa jadawalin shirye-shirye, za a kammala ne a ranar 17 ga wata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China