in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal: Macky Sall ya kaddamar da katin kasa na tantance fuska na kungiyar ECOWAS
2016-10-05 12:40:27 cri
Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya kaddamar a ranar Talata a birnin Dakar, da katin kasa na tantance fuska na kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS).

Kungiyar ECOWAS dake kunshe da kasashe goma sha biyar ce ta bayar da bayanai dalla dalla game da tsaro da kariya kan wannan katin tantance fuska.

Akwai dukkan muhimman bayanai da ake bukata kan wannan kati na kowane dan kasa, in ji mista Sall gaban 'yan jarida.

Haka kuma ya jaddada cewa wannan sabon katin tantance fuska za a yi amfani da shi kuma a matsayin katin zabe, kana zai taimakawa al'ummomin kasashe mambobi wajen gudanar da harkokin shige da fice a yankin ECOWAS tare da tantance su cikin sauki.

A cewarsa, sabon canjin da aka kawo shi ne ba za a iya satar fasaha ko yin jabu ba tare da wannan sabon katin tantance fuska ba.

An tsaida wa'adin fara aiki da wannan katin a shekarar 2017. Kuma za ta aiki bisa tsawon shekaru goma, katin na dauke da wata karamar na'ura mai kula da ayyukan daban daban. Katin zai maye gurbin katin zaman kasa na dole domin mutanen da ke da bukatar tsaya wa cikin wata kasar da ba tasu ba har fiye da watanni uku a cikin kungiyar ECOWAS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China