A yayin bikin mika tutar kasa ga rukunin, babban komandan jandarman, Jean Baptiste Tine, ya jaddada cewa bayan wani horon da ya basu damar kwarewa tare da tsarin aikin MDD da kuma yanayin ayyukan tabbatar da zaman lafiya, rukunin sojojin kasar Senegal na goma sha daya dake hanyar zuwa RDC-Congo ya shirya sosai wajen tafiyar da aikinsa yadda ya kamata.
Sojojin sun samu kwarewar da za ta ba su damar shiga ayyukan 'yan sandan MONUSCO. Muhimman ayyukansu za su hada da ba da kariya ga fararen hula, tabbatar da zaman lafiya da maido da ikon kasa, kawo gyaran fuska ga bangaren tsaro da kuma tallafawa ayyukan zabuka idan akwai bukata, in ji komandan Tine.
Hafsan ya kuma bukaci mambobin wannan rukuni da su girmama dokokin da ake bi wajen gudanar da ayyukan al'ummar Congo, musammun ma girmama al'ummomin kasar da kuma shugabannin kasar, tare da sanya kwarewarsu a sahun gaba. (Maman Ada)