in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Senegal ya ce kasar Sin ita ce kasa ta biyar a fannin huldar cinikayya da kasar Senegal
2016-11-28 13:04:43 cri
Ministan ciniki na kasar Senegal mista Alioune Sarr ya bayyana a ranar Lahadi, a yayin bikin bude taron baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ka gudana a birnin Dakar, cewa kasar Sin ita ce kasa ta biyar a duniya a fannin huldar cinikayya da kasar Senegal.

A cewar jami'in, cikin kasashen dake da huldar ciniki da Senegal, a baya kasar Sin ce ta 24, amma yanzu ta haura zuwa na matsayi na biyar, saboda kasar Senegal tana sayar da karin kayayyakinta zuwa kasar Sin.

Yayin da yake tsokaci game da dalilin samun wannan ci gaba, ministan ya ce manufar kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kokarin samun karuwar cinikayya tsakanin kasashen 2. A cewarsa, daga shekarar 2008, kasar Sin ta soke karbar harajin kwastam kan wasu kayayyakin da kasar Senegal take fitarwa, musamman ma wasu albarkatun noma da na teku. Matakin, a cewar jami'in, ya taimaka wajen raya wasu sana'o'i a kasar Senegal, tare da ciyar da tattalin arzikin Sin gaba.

Tun bayan da Sin da Senegal suka maido da huldar diplomasiya tsakaninsu a shekarar 2005, bangarorin 2 suna ta kokarin zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin Sin ta fitar sun sheda cewa, yawan kudin kayayyakin da aka yi cinikinsu tsakanin kasashen 2 a shekarar 2015 kadai ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 2.3. Haka zalika, karkashin tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, gwamnatin Sin ta kara kokarin tallafawa takwararta ta kasar Senegal, inda ta soke haraji kan kayayyakin kasar Senegal fiye da dubu 1, gami da kaddamar da ayyukan tallafi daban daban don amfanawa kasar Senegal.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China