in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a iya tabbatar da rasuwar babban jagoran IS ba, in ji shugaban hukumar tsaron kasa ta Amurka
2017-07-15 13:54:52 cri
Shugaban hukumar tsaron kasa ta Amurka James Mattis ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Amurka ba ta tabbatar da rasuwar babban jagoran kungiyar IS wato Abu Bakr al-Baghdadi ba.

A yayin taron manema labaran da aka yi a jiya, James Mattis ya ce, bisa manufar kasar Amurka, ana iya cewa, Abu Bakr al-Baghdadi bai rasu ba, har sai an sami shaidar da za ta tabbatar da rasuwarsa. Amma, kawo yanzu, rundunar sojojin Amurka ba ta kai ga samun iri wannan shaida ba.

Rahotanni daga kasar Iraki na cewa, IS ta riga ta yarda da cewa babban jagoranta Abu Bakr al-Baghdadi ya mutu, inda ta ce za a zabi sabon jagora nan bada jimawa ba.

Bayan kungiyar IS ta mamaye birnin Mosul na kasar Iraki a shekarar 2014, Abu Bakr al-Baghdadi ya sanar da kafauwar wata Daular da za ta keta kasashen Iraki da Syria. Amma rahotanni sun ce Baghdadi ya gudu daga birnin Mosul, inda aka boye shi a wani wurin dake kan yankin iyaka dake tsakanin kasashen Iraki da Syria.

A ranar 10 ga wannan wata ne Firaministan kasar Iraki ya sanar da cewa, an hambarar da jagorancin Abu Bakr al-Baghdadi tare da 'yanto dukkan birnin Mosul. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China