in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya yi Allah wadai da harin ta'addanci a Bagadaza
2017-05-31 10:04:21 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da kakkausan harshe game da harin ta'addanci da aka kaddamar a birnin Bagadaza na kasar Iraq.

A ranar Talata ne, aka kaddamar da harin ta'addancin a birnin na Bagadaza wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane 11 tare da raunata wasu 35.

Harin dai ya zo ne bayan wani makamancinsa cikin wata mota 'yan sa'o'i kadan bayan harin na farko, bugu da kari, wannan harin ya yi sanadiyyar hallaka mutane 11 da jikkata wasu 75. Kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islam ita ce ta dauki alhakin kaddamar da harin.

A ta bakin Stephane Dujarric, mai magana da yawun sakataren na MDD, Guterres, ya aike da sakon ta'aziyyar ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su. Kana ya yi fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.

Dujarric, ya jaddada cewa MDD tana cigaba da nuna goyon bayanta ga gwamnati da al'ummar Iraqi a kokarinsu na yaki da ayyukan ta'addanci da kuma zakulo wadanda ke da hannu domin gurfanar da su a gaban shari'a.

Hare haren dai sun faru ne a lokaci guda a daidai lokacin da jami'an tsaron Iraqi dake samu goyon bayan gamayyar kasa da kasa ke cigaba da fatattakar mayakan na IS a muhimmin garin dake hannunsu a yammacin birnin Mosul a arewacin Iraqi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China