in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka sun ce ba za su iya tabbatar da rasuwar babban jagoran IS ba
2017-07-12 10:51:47 cri
Rundunar sojojin kasar Amurka ta ce ya zuwa yanzu ba za ta iya tabbatar da rasuwar babban jagoran kungiyar nan ta IS, wato Abu Bakr al-Baghdadi ba.

Babban kwamandan sojojin Amurka dake kasar Iraki, Stephen Townsend ya fadawa 'yan jaridu a jiya Talata cewa, duk da sojojin Amurka sun samu bayanai ta hanyoyi daban-daban, amma kawo yanzu ba za a iya tabbatar da rasuwar Baghdadin ba.

Townsend ya kuma ce, a watan da ya gabata, akwai kafofin watsa labaran kasar Rasha, wadanda suka ruwaito cewa, kila Baghdadin ya mutu sakamakon luguden wutar da sojojin Rasha suka yi a Syria, amma bisa bayanan da sojojin Amurka suka samu, wannan ba gaskiya ba ne.

Rahotanni daga kasar Iraki sun ce, IS ta rigaya ta yarda cewa, babban jagoran kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi ya mutu, kana ta ce za'a zabi sabon jagora nan bada jimawa ba. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China