in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Syria sun kaddamar da wani sabon yaki da kungiyar IS mai taken 'Great Dawn'
2017-05-27 13:21:35 cri

Wata majiya daga Rundunar sojin Syria, ta ce rundunar tare da kawayenta, sun kaddamar da sabon yaki da kungiyar IS mai taken "Great Dawn" a yankuna da dama na kasar ta Syria.

Dakarun sun fara aikin ne cikin kwanaki biyu da suka gabata, inda suka samu kwato murabba'in kilomita 13,000 a yankin tsakiyar kasar, galibi a lardin Homs dake yankin kudu maso gabashin kasar da kuma yanki mai tsaunuka na Qalamoun dake arewa maso yammacin birnin Damascus.

Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce wannan aiki shi ne mafi girma tun bayan kaddamar da yaki kan kungiyar IS shekaru 6 da suka gabata.

Dakarun na Syria da kawayensu, sun kutsa yankunan da mayakan IS suka mamaye a yankin Homs dake kudu maso gabashin kasar, inda suka kwace iko da muhimman yankuna daga hannun kungiyar.

Farmakin na dakarun ya kuma ba su damar kwace babbar hanyar dake tsakanin birnin Damascus da daddaden garin Palmyra.

Munufar farmakin ita ce, cin galaba a kan kungiyar IS a yankin sahara dake tsakiyar kasar Syria tare da kwace yankunan dake kusa da iyakokinta da Jordan da Iraqi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China