in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta dauki alhakin kaddamar da harin birnin London
2017-06-05 10:01:50 cri
Kungiyar dake da'awar kafa daular musulunci(IS) ta dauki alhakin kaddamar da harin da aka kai ranar Asabar a birnin London, harin da ya yi haddasa mutuwar mutane 7 kana wasu 48 kuma suka jikkata, ciki har da wasu 21 da ke cikin matsanancin hali.

Kafar yada labarai da BBC ta wallafa a shafinta na intanet cewa, sashen watsa labarai na kungiyar mai suna Amaq ya wallafa a manhajar aikewa da sakonnni na Telegram cewa, sashen tsaron mayakan kungiyar ne ya kaddamar da harin na London.

Rundunar 'yan sandan Burtaniya dai ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an kama mutane 12 da ake zargin suna da hannu a wannan hari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China