in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugban kasar Chadi ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin
2017-05-10 11:06:18 cri

A jiya Talata, shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao a N`Djamena , fadar mulkin kasar Chadi.

A yayin ganawar tasu, Li Yuanchao ya ce huldar dake tsakanin Sin da Chadi na samun ci gaba cikin sauri a shekarun baya, inda suka samu nasarori da yawa kan hadin gwiwarsu mai amfanin juna. Ban da haka kuma, shugabannin kasashen 2 sun yi ganawa a bara, inda suka samar da cikakken shirin ga yadda bangarorin 2 za su yi hadin kai a fannoni daban daban a nan gaba, tare da tabbatar da alkiblar da za a bi domin kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.

Li ya ce makasudin ziyararsa shi ne domin tabbatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma, da musayar ra'ayi tare da bangaren Chadi kan yadda za a aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla a taron koli na Johannesburg karkarshin laimar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka.

A nasa bangaren, shugaba Deby na kasar Chadi ya ce, ya sha ganawa tare da shugaba Xi Jinping na kasar Sin a lokuta da dama, inda suka cimma matsaya daya kan hadin gwiwar Sin da Chadi a fannoni daban daban. A cewarsa, Chadi na kallon dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin da muhimmanci matuka, kuma ta riga ta amince da manufar kasar Sin ta yin hadin gwiwa don amfanin juna. Saboda haka kasar na son karfafa huldar hadin kai da abokantaka tare da kasar Sin.

Yayin da yake ziyara a kasar Chadi a wannan karo, mataimakin shugaban kasar Sin shi ma ya gana da firaministan kasar Chadin Albert Pahimi Padacke, inda suka ganewa idonsu kan yadda aka sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi na hadin kai, tare da rangadi ga wasu ayyuka na hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China