Mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya bayyana aniyar kasarsa na yin aiki tare da kasar Singapore da nufin samar da sabbin damammakin da za su kai ga bunkasa tare da daga matsayin hadin gwiwar kasashen biyu gaba.
Mr Li ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya ke gabatar da sakon shugaba Xi Jinping yayin da ya halarci bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kasar Singapore a matsayin manzon shugaba Xi.
Ya kara da cewa, kasashen biyu sun kulla sabbin hadin gwiwa a fannonin da suka shafi harkokin kudi, Kimiyya, harkar ilimi, harkokin tafiyar da mulki da inganta rayuwar jama'a da dai sauransu. Kuma kasar ta Sin tana fatan kara inganta hadin gwiwar manyan tsare-tsare da kasar ta Singapore.
Mataimakin shugaban kasar na Sin ya kuma bayyana cewa, tun lokacin da sassan biyu suka kulla huldar diflomasiya shekaru 25 da suka gabata, huldar cinikayya da zuba jari da ke tsakaninsu ke bunkasa sannu a hankali.
A nasa jawabin Firaministan kasar Singapore Lee Hsien Loong ya bayyana godiya da yadda shugaba Xi ya aiko da manzo na musamman don ya halarci bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kan kasar. Ya ce, Singapore a shirye take ta yi amfani da shekaru 25 na kulla huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu don kara inganta dangantaka a tsakaninsu.
Ya bayyana cewa, Singapore za ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta dangantaka a tsakanin kungiyar ASEAN da kuma Sin a ko wane lokaci.
A yayin da yake kasar ta Singapore Li Yuanchao ya kuma gana da shugaba Tony Tan Keng Yam da mataimaikin firaminista da kuma mninistan kudin kasar ta Singapore Tharman Shanmugaratnam.(Ibrahim)