in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin
2017-05-09 09:50:35 cri

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya gana da Li Yuanchao, mataimakin shugaban kasar Sin, a Dakar fadar mulkin kasar Senegal a jiya Litinin.

Yayin ganawar, Li Yuanchao ya ce, kasashen Sin da Senegal kawaye ne masu hulda ta kut-da-kut.

Yayin taron koli na kungiyar G20 da ya gudana a birnin Hangzhou na kasar Sin, shugabannin kasashen 2 sun cimma daidaito wajen kara kyautata huldar dake tsakaninsu, ta yadda kawancen zai zurfafa hadin gwiwarsu kan manyan tsare-tsare da wasu bangarori daban-daban.

A cewar jami'in na kasar Sin, ya kai ziyara kasar Senegal a wannan karo ne musamman don gudanar da ayyukan da aka tanada cikin yarjejeniyar da shugabannin kasashen 2 suka cimma, don amfanin jama'ar kasashen 2.

A nasa bangare, Macky Sall ya mika sakon gaisuwa da goron gayyata ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, yana mai cewa, huldar dake tsakanin Senegal da Sin ta dace da bukatun kasarsa ta fuskar neman ci gaban.

A sabili da haka, Senegal ta na kallon kasar Sin a matsayin aminiya da za ta rika hadin gwiwa da ita.

A ziyararsa ta yini 2 a Senegal, mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da firaministan kasar Mahammed Dionne, tare da gane wa idanunsa yadda aka kulla wasu yarjeniyoyi na hadin kai tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China