in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taro na 41 na kwamitin kula da kayakin tarihi na duniya inda aka yi kira da kara ba wuraren tarihi kariya
2017-07-13 13:22:53 cri

An kammala taro na 41 na kwamitin kula da wuraren tarihi na duniya na hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu na MDD a jiya Laraba a birnin Krakow dake kudancin kasar Poland.

Taron wanda aka fara daga ranar 2 zuwa 12 ga watan Yuli ya sanya sabbin wurare 21 cikin jerin wuraren tarihi na UNESCO, inda ya hada da wuraren al'adu 18 da muhallin halittu 3, wanda ya kawo jimilar wuraren zuwa 1,073.

Baya ga Gulangyu na kasar Sin mai cike da tarihi da Hoh Xil shi ma na kasar Sin wanda ya kasance tsauni mafi girma a duniya, akwai wasu wurare na Turkiyya da Eritrea da Hebron da Argentina da Dauria da Indiya da Japan da Angola da Iran da Rasha da Jamus da Poland da Cambodia da Afrika ta Kudu da Croatia da Italy da Montenegro da Faransa da Burtaniya da Brazil da kuma Greenland da suka shiga cikin jerin wuraren.

Kawo yanzu, kasar Sin na da 52 cikin jerin, yayin da wuraren kasar Angola da Eritrea suka shiga a karon farko. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China