in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan dawo da karin kayan tarihin ta gida
2017-02-16 20:21:03 cri
Mahukuntan kasar Sin sun kuduri aniyar dawo da karin kayan tarihin kasar da aka fice da su zuwa kasashen ketare. Karkashin wannan manufa, za a bude shafin yanar gizo na musamman, wanda zai rika yada bayanai game da irin wadannan kayayyaki na tarihi, domin cimma burin maido su kasar ta Sin.

Kamfanin dillancin labarai na Sin Xinhua, ya hakaito hukumar kasar Sin mai lura da kayayyakin da aka gada daga kaka da kakanni ko (SACH) na cewa, wannan kuduri na cikin manyan ayyukan da ta sanya gaba a wannan shekara.

SACH ta kuma ce tana da aniyar daukar matakan inganta tsaron kayan tarihin na dauri, da kuma tsaurara hukunci ga wadanda suka karya dokar kare su. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China