Kwamitin kula da harkokin wuraren tarihi na kasa da kasa yana ganin cewa, a birnin Kulangsu, an hada da al'adu na iri daban daban na yankin Asiya tare, kuma ana iya ganin tsoffin gine-ginen da na zamanin yanzu irin na kasar Sin, na yankin Asiya ta kudu maso gabas, har ma da kasashen Turai a wannan wurin. Haka kuma, haduwar al'adu iri daban daban ta haifar da wasu al'adun na musamman a Kulangsu, musamman ma a fannin gine-ginen da aka fi sani da "kawatawar Xiamen", wanda ya kuma ba da tasiri ga wasu kasashen dake yankin Asiya ta kudu maso gabas, da dai sauran wurare masu nisa sosai.
Haka zakika, a yayin babban taron da aka yi a ranar Jumma'a da ta gabata, an shiga da Hoh Xil dake lardin Qinghai na kasar Sin cikin jerin wuraren tarihi na duniya. (Maryam)