A cikin wannan rahoto, an yi bincike game da kasashe da yankuna 141, da nazarin alkaluman su, don kyautata tattalin arziki, da babbar moriyar da sha'anin yawon shakatawa ke haifarwa.
A cikin rahoton, an ce, duk da kasancewar wadannan kasashe a sahun gaba cikin jerin sunayen kasashen da aka fi son zuwa yawon shakatawa, wato Spaniya, Faransa, Jamus, Amurka, Birtaniya, Swiss, Australiya, Italiya, da Canada, a hannu guda irin gibin da ke akwai tsakanin kasashe masu wadata, da gamayyar tattalin arzikin kasashen masu saurin bunkasuwa na raguwa.
Kaza lika rahoton ya nuna cewa, lokacin da ake samun karin masu yawon shakatawa a duniya, da karuwar masu kudi, yankin gabashin Asiya shi ma, ya zama wurin da masu yawon shakatawa suka fi ziyarta. (Bako)