in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar UNWTO ta jinjinawa shirin kawar da talauci ta hanyar raya yawon shakatawa na kasar Sin
2015-08-05 14:09:21 cri

Kungiyar yawon shakatawa ta duniya (UNWTO), ta fidda wata sanarwa a jiya Talata, inda ta jinjinawa shirin da kasar Sin ta yi na kawar da talauci ta hanyar raya aikin yawon shakatawa a kauyuka.

Sanarwar ta ce, sakataren kungiyar UNWTO Taleb Rifai ya zanta tare da hukumomi masu kula da aikin yawon shakatawa na kasar Sin, inda ya jinjinawa shirin rage kashi 17 cikin dari na duk yawan matalautar kasar Sin ta hanyar tsara raya aikin yawon shakatawa.

Sanarwar ta ruwaito Taleb Rifai na cewa, raya aikin yawon shakatawa zai iya rage yawan matalauta da ingiza bunkasuwar kauyuka, matakin da zai samar da karin guraban ayyukan yi. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China