Mahukuntan birnin Zhengzhou dake lardin Henan na tsakiyar kasar Sin, sun bayyana shirin su na zuba zunzurutun kudi har Yuan biliyan 9.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.4, tsakanin shekarun 2017 zuwa 2020, domin gina wasu wurare 75 masu kunshe da shuke shuke da za su shafe murabba'in sakwaya mita miliyan 33, wadanda za a yi amfani da su wajen kare martabar kayan tarihin dake birnin.
Gine ginen da za a fara cikin wannan shekara ta 2017, za su kunshi wuraren shakatawa 17.
Ana sa ran kyawawan muhallan halittu, da wuraren shakatawar, za su ba da wata dama ta fadada wuraren jin dadin jama'a, da na inganta rayuwar halittu daban daban.
Birnin Zhengzhou dai na cikin tsaffin manyan biranen kasar Sin guda 8, yana kuma dauke da wuraren tarihi sama da 10,000, ciki hadda tsaffin gine ginen gargajiya 6, wadanda ke cikin muhimman wurare da ake karewa. A kuma fannin tarin kayan tarihi na dauri, birnin shi ne na farko a dukkanin fadin kasar Sin.(Saminu)