An cimma wannan ne a jiya Jumma'a, yayin babban taro da hukumar ta kira kan wuraren tarihi da al'adu da kayayyakin da aka gada daga kaka da kakanni da ya gudana a birnin Krakow na kasar Poland.
Zuwa yanzu, akwai jimilar wurare 51 na kasar Sin wadanda ke cikin jerin wuraren tarihi na duniya.
Wannan wurin tarihi, wato Hoh Xil mai fadin gaske, ya kunshi manyan tabkuna da dabbobi da halittu.
Kungiyar kare wuraren tarihi ta duniya ta fitar da wani rahoto, inda ta ce, Hoh Xil na da fadin sosai, wanda kuma ko kadan ayyukan dan Adam ba su tasiri kansa ba, kana kyan wurin abun burgewa ne matuka.
Har wa yau, rahoton ya ce a wannan wuri, akwai wani nau'in musamman na barewa irin ta kasar Sin, inda suke zirga-zirga ba tare da wata matsala ba.(Murtala Zhang)