An bude dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar wasu birane gami da kananan hukumomi na kasashen BRICS
Yau Laraba da safe, a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, aka kaddamar da taron dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar wasu birane, gami da kananan hukumomi na kasashe membobin kungiyar BRICS, inda wakilan gwamnatoci daga Rasha, Brazil, Indiya, gami Afirka ta Kudu, tare kuma da wakilai, da kwararru, da masana na gwamnatocin wasu jihohi da birane na kasar Sin suka hallara, domin yin shawarwari kan yadda za'a inganta hadin-gwiwa tsakanin birane da kananan hukumomi na kasashen BRICS.
Mataimakin shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, Wang Jiarui, ya gabatar da jawabin dake cewa, ta hanyar inganta hadin-gwiwa tsakanin al'umma da birane da kuma kananan hukumomi, za'a taimaka wajen raya ayyukan diflomasiyya na kasashe mambobin kungiyar ta BRICS. Har wa yau, kasar Sin na maida hankali sosai kan hadin-gwiwa, da mu'amala tare da sauran kasashen BRICS, domin neman samun moriya tare.(Murtala Zhang)