Wakilai daga kasashe mambobin kungiyar BRICS, sun amince da wani tsari, wanda zai ba su damar bunkasa hadin gwiwa tsakanin su a fannin musayar al'adu. Wakilan sun bayyana hakan ne yayin taron su na Alhamis din nan, wanda ya gudana a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin.
A madadin kasashen su, mahalarta taron sun alkawarta daukar karin matakai, wadanda za su bada damar karfafa musayar al'adun na su, tare da kare ababen da aka gada daga kaka da kakanni.
Sauran sassan da shirin ya kunsa, sun hada da bada horon kwarewa da sanin makamar aiki tsakanin kasashen na BRICS. Sai kuma karfafa gwiwar juna wajen adana kayan tarihi da dakunan karatu, duka dai da nufin fadada musaya a fannin kare al'adun juna, ta hanyar nune nune da musayar bayanai.(Saminu Alhassan)