Yau Laraba 5 ga wata ne aka kaddamar da taron ministocin ilmi karo na biyar na kasashe mambobin kungiyar BRICS a nan birnin Beijing, taron da aka yiwa take da "hadin gwiwar kasashe mambobin BRICS don cimma adalci da kyautatuwa a fannin ilmi".
A yayin wannan taro, an rattaba hannu kan Sanarwar aikin koyarwa ta Beijing, da ma sauran wasu yarjeniyoyi, kana an cimma daidaito kan hadin gwiwar kasashen kungiyar a fannin bunkasa ilmi a nan gaba. (Kande Gao)