in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS na fatan hada kai da sauran kasashe wajen raya makomar dan Adam tare
2017-06-20 20:13:11 cri

A ranar 20 ga watan nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Gan Shuang ya bayyana a yayin taron manema labaru a nan Beijing cewa, har kullum burin kasashen BRICS ne su hada kansu, domin neman samun nasara tare bisa tunanin bude kofa ga kowa.

Mr. Gan ya ce kasashen kungiyar ba sa nemi kafa kawancen siyasa da aikin soja domin wata kasa. Kaza lika ba sa nemi kalubalatar wata kasa ta daban, sannan kuma ba sa nemi maye gurbin wata kasa. Abun da kawai suka sanya baya shi ne hada kai da sauran kasashe, wajen raya makomar dan Adam tare.

A ranar 19 ga watan nan ne aka yi taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS a nan Beijing, inda ministocin harkokin wajen kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin, da Afirka ta Kudu, suka tattauna kan halin da ake ciki a duniya, da batutuwan shiyya-shiyya da na kasa da kasa da ke jawo hankalin sassa daban daban. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China