in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da ministocin harkokin wajen Rasha, Afirka ta Kudu, Brazil da Indiya
2017-06-19 17:54:46 cri

Yau Litinin ne a nan Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya gana da ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, da Afirka ta Kudu, da Brazil da Indiya yayin da suke halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS.

Da yake zantawa da su, shugaba Xi ya ce yanzu haka shekaru 10 sun shude tun bayan fara aiki da tsarin hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS. Don haka ya zama wajibi a ci gaba da yin hadin gwiwa tare da samun nasara tare a tsakanin kasashen kungiyar ta BRICS, a bi tsarin "tattaunawa tare, da samun ci gaba tare, da kuma cin gajiya tare". Sa'an nan a ci gaba da tsayawa tsayin daka, kan raya hulda a tsakanin kasa da kasa.

Shugaban kasar Sin ya kara da cewa, muddin kasashen BRICS sun hada kansu da zuciya daya, lallai hadin gwiwar ta su zai kara bunkasa, kuma kasashen 5 za su samu nasara nan da shekaru 10 masu zuwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China