in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya ja hankalin kungiyar BRICS game da daukar matakan bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya
2017-07-07 19:17:16 cri

Suhugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatarwa jagororin kasashe kungiyar BRICS, shawarar daukar kwararan matakan bunkasa tattalin arzikin duniya cikin hadin giwa, da bude kofa ga juna, tare da bunkasa ci gaban dukkanin sassa, domin cimma moriya tare.

Shugaban na Sin ya gabatar da wannan shawara ne, yayin wani kwarya kwaryar taro, na shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, wadanda suka hada da Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da kuma Afirka ta kudu, gabanin bude taron kungiyar G20 wanda yanzu haka ke gudana a birnin Hamburg na kasar Jamus.

Shugaba Xi tare da sauran shugabannin kungiyar dai sun yi musayar ra'ayoyi, game da yanayin da ake ciki don gane da wasu muhimman batutuwa da suka shafi siyasar kasa da kasa, da batun tattalin arziki, tare da muhimman kudurorin da kungiyar G20 ta sanya gaba.


1  2  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China