in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar kungiyar BRICS na samun karin tagomashi
2017-06-19 20:40:00 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar BRICS na samun karin tagomashi.

Mr. Wang ya bayyana hakan ne a yau Litinin, yayin da yake jawabi wajen bude taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar ta BRICS, taron da ya samu halartar Mr. Sergey Lavrov daga Rasha, da ta Afirka ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane, da na kasar Brazil Aloysio Nunes, da kuma na India Vijay Kumar Singh.

Ministan na harkokin wajen kasar Sin ya kara da cewa, hadin gwiwar kasashen kungiyar na da tasirin gaske, duba da cewa kasashen dake cikin kungiyar na da kaso mafi tsoka bisa jimillar tattalin arzikin duniya, inda a cikin shekaru 10 na baya bayan nan, adadin da suke da shi ya karu daga kaso 12 zuwa 23 cikin dari, yayin da a hannu guda suke mallakar sama da rabin ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Ya ce a bana an bude sabbin shekaru 10 a tarihin hadin gwiwar kasashen kungiyar ta BRICS, kuma kasar Sin ce ke rike da jagorancin karba karba na kungiyar a yanzu, don haka Sin za ta yi tsaiwar daka tare da sauran sassa domin tabbatar da wanzuwar daidaito, da kuma ci gaba mai dorewa da hadin kai tsakanin daukacin sassan duniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China