in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 22 sun gamu da ajalinsu a harin da aka kai a Manchester
2017-05-23 20:01:32 cri

 

Rundunar 'yan sandan birnin Manchester ta sanar da cewa, mutane 22 ciki har da yara ne suka mutu, kana wasu 59 kuma suka jikkata sakamakon wani harin kunar wake da aka kai jiya da dare a filin wasa na Manchester dake Ingila.

Sanarwar da rundunar 'yan sandan Greater Manchester ta bayar ta ce ta yi imanin harin da wani mutum guda ya kaddamar, hari ne na ta'addanci.

Babban jami'in 'yan sandan Greater Manchester Ian Hopkins ya tabbatar da cewa, maharin ya mutu a filin wasan kuma yana dauke da wani abin fashewa ne wanda ya haddasa wannan danyen aiki.

Sanarwar ta bayyana cewa, yanzu haka ana jinyar wadanda suka jikkata a asibitoci guda takwas dake sassa daban-daban na birnin Manchester.

Wani labari da dumi-dumi dake shigo mana na cewa, kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi ta sanar da daukar alhaki kan wannan harin.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China