Da yake ganawa da manema labarai, Zhu ya ce taron na da matukar muhimmanci ga mambobi su tabbatar da tsara harkokin kudi da na tattalin arzikin kasashensu da inganta amfani da dabarun kula da hada-hadar takardar kudade ta yadda za su rike darajarsu da kula da harkokin kudaden shiga da wanda suke kashewa tare da tabbatar da sauye-sauye don samun dorewar ci gaban tattalin arzikin duniya.
Ya ce a matsayin kasar Sin na mai goyon bayan bunkasar tattalin arzikin duniya, ta hannun shawarar "ziri daya da hanya daya" da karfafa hadin kai ta yadda za a samar da makoma mai kyau ga dukkan bil'adama, a shirye take ta yi aiki da bangarori daban-daban na fadin duniya don samar da moriya ga al'ummar duniya.
Ya ce a fannin harkokin kudi kuwa, ma'aikatar kudi da babban bankin Jamus sun gabatar da wasu batutuwa uku da suka hada da karfafa tattalin arziki da inganta harkokin zuba jari musammam a nahiyar Afrika da kuma zamanantar da harkokin tattalin arziki, wandanda batutuwa ne da aka tattauna kansu yayin taron bara da ya gudana a Hangzhou, inda suka samu goyon bayan kasar Sin da sauran kasashe mambobin kungiyar G20. (Fa'iza Mustapha)